BBC navigation

Kamfanin mai na Shell zai gurfana a gaban kuliya

An sabunta: 11 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 08:00 GMT
Malalar mai a yankin Niger Delta a Najeriya

Malalar mai a yankin Nigerb Delta mai arzikin man petur a Najeriya

Idan an jima a yau ne wakilan katafaren kamfanin mai na Shell, za su gurfana gaban kuliya a kasar Netherlands, don fuskantar zargin gurbata muhalli a Nigeria, saboda karar da wasu manoma hudu daga yankin Niger Delta mai arzikin man fetur suka shigar gaban kotun.

Manoman sun ce malalar mai da kamfanin na Shell ya haddasa ya lalata musu amfanin gona da aiyukansu na kamun kifi.

A nasa bangare, kamfanin Shell ya ce yawancin malalar mai dake faruwa a yankin, barayin mai ne da masu yiwa kamfanin zagon kasa, ke haddasa shi.

Manoman wadanda wani bangaren kamfanin mai na Dutch dake lura da muhalli ke mara wa baya, da aka fi sani da ''Friends of the Earth'', na bukatar kotun ta tilasta wa kamfanin Shell ya dakatar da malalar man, tare da biyansu diyya.

Kamfanin mai na Shell dai ya musanta zargin da cewa fiye da rabin malalar man na faruwa ne sakamakon zagon kasar da ta ce masu lalata bututu da satar man ke yi a yankin.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.