BBC navigation

An sace Kambin sarkin Ashanti

An sabunta: 12 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 15:10 GMT
Sarkin Ashanti, Ghana

Sarkin Ashanti, Ghana

Da alamu 'yan kabilar Ashanti dake kasar Ghana sun fara nuna damuwa dangane da makomar sarkinsu wato Asantehene Osei Tutu, bayan da a jiya aka sace mashi kambin sarautarsa a wata ziyarar da ya kai a kasar Norway.

Rahotannan dake fitowa daga Norway din dai sunce an sace kambin na zinariya ne a hotel din da sarkin tare da tawagarsa suka sauka a birnin Oslo.

Kambin dai na cikin abubuwa mafi daraja a cikin kayan sarautar Daular Ashanti dake cikin daulolin da suka fi fice da kuma daraja a nahiyar Afrika.

Yanzu haka kuma gwamnatin kasar ta Norway ta ce bata da wani taimako da zataiwa sarkin domin gano kambi sabilida ba ita ce ta gayyace shi zuwa kasar ba.

Ko da yake rahotanni sun ce 'yan sandan kasar sun ce suna gudanar da bincike kan wani hotan talabijin da ke cikin otel din wnda ya nuna wani mutum da ya dauki akwatin da kmbin ke ciki.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.