BBC navigation

Syria ta zargi Fira Ministan Turkiyya da yin karya

An sabunta: 12 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 07:29 GMT
Jirgin saman Syria a kasar Turkiyya

Jirgin saman Syria a kasar Turkiyya

Syria ta zargi Fira Ministan kasar Turkiyya, Recep Tayyib Erdogan da yin karyar cewa jirgin saman kasar Syria da aka tilastawa sauka a Ankara ranar Laraba na dauke da makamai da sauran kayayyakin aiki na soji.

Ma'aikatar Harkokin wajen kasar dake birnin Damascus ta kalubalanci Mr Erdogan da ya fito ya nuna kayayyakin da ya ce an kwace a bainar jama'a.

Kasar Turkiyyar dai ta kama jirgin ne saboda tana zargin an keta dokar hana shigo da makamai.

A baya-bayan nan dai Ma'aikatar Harkokin wajen Rasha ta ce kama jirgin da kasar Turkiyyar ta yi ya saka rayuwar fasinjoji cikin hatsari, inda ta kuma ta shaidawa BBC cewa baya dauke da wasu makamai ko dangoginsa.

Kananan jiragen yakin kasar Turkiyya ne suka tilastawa jirgin saman fasinjan kasar Syriyar sauka a filin saukar jiragen saman Ankara, a bisa zargin cewa yana dauke da muggan makamai na gwamnatin Syria.

Sai dai jami'an gwamnatin Turkiyyar ba su bayyana takamaiman abinda suka gano ba a lokacin da suka binciki jirgin da ya taso daga birnin Moscow.

Ministan Harkokin wajen Turkiyya Ahmet Davutoglu ya ce an kyale jirgin ya wuce da fasinjojin amma ba tare da wasu daga cikin kayayyakin da ya ke dauke da su ba, domin ci gaba da tsare jirgin zai haifarwa da fasinjojin damuwa.

Kasar Turkiyyar dai ta ce za ta ci gaba da bincike ne kan wadannan kayayyaki da ta kama a cikin jirgin na kasar Syria da ta ce akawi ayar tambaya a kai, duk da kuwa ci gaba da musantawar da Ma'aikatar harkokin wajen Syriyar ke yi na cewa jirgin na su baya dauke da wasu makamai.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.