BBC navigation

Ana taron kasashe masu amfani da harshen Faransanci a Congo

An sabunta: 13 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 20:12 GMT
Shugaba Hollande na Faransa

Shugaba Hollande na Faransa

A jamhuriyar dimukradiyyar Congo an bude taron kasashen dake amfani da harshen Faransanci, a daidai lokacin da ake kara nuna damuwa damuwa dangane da tashin hankali a gabashin jamhuriyar dimukradiyyar Congon da kuma kwace iko da yankin arewacin Mali da masu kaifin kishin Islama suka yi.

Faransa dai ta bada goyon baya ga kai daukin dakarun kasashen waje a kasar ta Mali, kuma tuni kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya ya bukaci kasashen yammacin Afurka su gabatar da cikakken tsari kai daukin soja a kasar ta Mali.

Shugaban kasar Faransa, Francois Hollande ya fadawa taron cewa, Faransa tana goyon bayan daukar matakin soja a arewacin Mali.

Daya daga cikin kungiyoyin 'yan kishin Islamar a kasar Mali sun ce a sakamakon goyon bayan da Mr hollande ya nuna kan tura sojoji Mali, ya sa ransa da kuma na 'yan kasar Faransa da ake garkuwa da su cikin hadari.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.