BBC navigation

Dogarin tsohon shugaban Ivory Coast zai daukaka kara

An sabunta: 13 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 08:00 GMT
Dakarun Majalisar Dinkin Duniya a Ivory Coast

Dakarun Majalisar Dinkin Duniya a Ivory Coast

Lauyan da ke kare dogarin tsohon shugaban kasar Ivory Coast Laurent Gbagbo ya ce mutumin da yake wakilta na shirin daukaka kara a kan hukuncin da aka yanke masa na shekaru 15 a gidan yari bisa zarginsa da aikata kisan kai.

A shariar da aka yi ta farko kan rikicin da ya biyo bayan zaben kasar, an yanke wa Janar Bruno Dogbo Blé hukuncin ne saboda samunsa da hannu a halaka wani tsohon hafsan soja a watan Maris na bara.

Jaridun da ke goyon bayan gwamnatin kasar sun bayyana hukuncin da cewa an yi sassauci sosai a cikin sa, yayinda jaridun dake goyon bayan tsohon shugaban kasar Mr Gbagbo, suka ce rufa-rufa kawai aka yi.

Wata jarida ta ce ya samu hukuncin daurin shekaru 15 a gidan yari saboda biyayyarsa ga Gbagbo.

Lauyan Janar Dogbo Ble' ya ce zai daukaka kara zuwa wata babbar kotun ne saboda kotun da ta yanke hukuncin ta kasa nuna wasu kwararan shedu da suka nuna cewar janar din ne ya bada umarnin hallaka kanar Meju Adama Doso.

Yace masu gabatar da kara na kotun majistire sun nemi a yanke masa hukuncin daurin shekaru 25 amma kotun ta yanke masa hukuncin daurin shekaru 15, bisa dalilin cewar babu kwararan shedu kan shari'ar, wanda abin mamaki ne.

An dai samu Janar Dogbo Ble' ne da laifin sacewa da tsare mutane ba bisa ka'ida ba da kuma kisan gilla.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.