BBC navigation

'Morocco ta sake lale akan daukar reinon yara'

An sabunta: 13 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 20:12 GMT

Sarkin Morocco

Wasu ƙungiyoyin agaji na ƙasar Morocco shida sun yi ƙira ga gwamnatin ƙasar ta sauya shawara dangane da hana musulmi 'yan ƙasashen waje ɗaukar renon yaran ƙasar da iyayensu suka yi watsi da su.

Cikin watan jiya ne dai ma'aikatar shari'a ta ƙasar haramtawa musulmi 'yan wasu ƙasashe ɗaukar rainon yaran ƙasar da aka yi watsi da su.

Wakilin BBC ya ce, ƙungiyoyin agajin da suka yi wannan ƙira ga hukumomin Morocco sun ce, a kowacce rana ana jefar da yara ƙanana ashirin da huɗu a ƙasar ta Morocco.

Kuma ƙungiyoyin suka ce, 'yan ƙasar ta Morocco kalilan ne suke ƙaukar rainon irin wadannan yara da ake jefarwa.

Ƙungiyoyin dai sun yi gargaɗin cewa idan ba an ɗauki matakan magance matsalar ba, akwai yuwuwar ƙungiyoyi na masu safarar mutane su shiga cikin lamarin, su kuma riƙa safarar ƙananan yara.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.