BBC navigation

Majalisar Dinkin Duniya ta amince da kudiri kan matakin soji a Mali

An sabunta: 13 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 06:48 GMT
Dakarun 'yan tawayen kasar Mali

Dakarun 'yan tawayen kasar Mali

Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya amince da kudirin da zai kai ga kusa da matakin yin amfani da tsoma bakin soji a kasar Mali.

Kwamitin ya yi kira ga kasashen Afirka ta yamma da su yanke shawarar su ta karshe game da wannan batu a cikin kwanaki 45, wanda zai taimaka wajen fatattakar 'yan tawaye masu kaifin ra'ayin addinin Islama da suka kwace ikon akasarin yankunan arewacin kasar, bayan wani yunkurin juyin mulkin da bai samu nasara ba a cikin watan Mayu.

Kudirin yayi nuni da damuwa kan yadda 'yan tawaye masu kaifin ra'ayin addinin Islama suka mamaye tare da karbe ikon yankuna masu dama a arewacin Mali.

Kudirin ya kuma nuna takaicinsa game da yanayin yadda kasashen Afirka ke tafiyar da yunkurin su kan rikicin dake faruwa.

Kasar Mali da Kungiyar Tattalin Arzikin Kasashen Afirka ta Yamma ECOWAS ne suka nemi izinin Majalisar Dinkin Duniya da ta yi amfani da dakarun kasa-da kasa karkashin jagorancin kasashen nasu da su kwato yankin arewacin na Mali, amma kuma a cikin watanni mambobin majalisar sun sha neman da a ba su cikakken tsarin yadda za a gudanar da aikin.

Kudirin dai wani yunkuri ne na kara zaburar da kungiyar ta ECOWAS.

Kasar Faransa ce ta tsara daftarin kudirin, ta yi ja gaba game da wannan batu saboda a matsayinta ta kasar da ta yi wa Mali mulkin mallaka, ta damu ainun kan kalubalen tsaro da barazanar da kasar ke fuskanta daga 'yan tawaye masu zazzafan ra'ayin addinin Islama.

Amincewa da kudirin na Majalisar Dinkin Duniya na zuwa ne mako guda gabanin wata ganawar da za a yi a Bamako babban birnin kasar Mali, da zai hada kawunan duka wakilan kungiyar ta ECOWAS, Kungiyar Tarayyar Afirka da kuma babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, domin tsara wasu sabbin matakai masu karfi na tunkarar matsalar da ke kara ta'azzara a kasar ta Mali.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.