BBC navigation

Najeriya: 'Yan fashi sun kashe mutane 22 a jihar Kaduna

An sabunta: 14 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 15:43 GMT
Jami'an tsaro a Nijeriya

Jami'an tsaro a Nijeriya

Jami'ai a Najeriya sun ce, wasu 'yan bindiga sun kashe akalla mutum ashirin da biyu a wani hari da suka kai ƙauyen Dogon Dawa dake jihar Kaduna yau da sanyin safiya.

An kashe kimanin mutane tara ne a masallaci.

Kwamishinan yaɗa labarun jihar Kaduna, Sa'idu Adamu ya faɗawa BBC cewa, gungun wasu 'yan fashi ne suka kai harin.

Ya kuma kara da cewa, 'yan bindigan sun kai harin ne domin mayar da martani ga ƙoƙarin 'yan banga na yankin dake hana su cigaba da addabar kauyen da hare-haren fashi da makami.

Rahotannin sun ƙara da cewa 'yan fashin, waɗanda yawansu ya kai kimanin ɗari, sun kashe wani basarake, makaman Birnin Gwari, Alhaji Ahmadu Aliyu a gidansa.

Shi ma kwamishinan 'yan sandan jihar ta Kaduna, Olufemi Adenaike ya tabbatar da rahotannin kai harin, amma ya ƙi ya ce uffan kan zargin cewa, an sanar da su barazanar 'yan fashin ta kai hare haren gabanin ƙaddamar da shi.

Kwamishinan 'yan sandan ya ce sun tura dakaru zuwa ƙauyen na Dogon Dawa a halin da ake ciki.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.