BBC navigation

Hatsaniyar 'yan kallo ta dakatar da gasar wasan kwallo a Senegal

An sabunta: 14 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 07:39 GMT
Dan wasan kwallon Ivory Coast

Dan wasan kwallon Ivory Coast

Hatsaniyar da 'yan kallon suka tayar a filin wasan Dakar ya tilasta dakatar da wasan kwallo tsakanin Ivory Coast da Senegal, wanda wani muhimmin wasan neman gurbi ne a Gasar cin Kofin Kwallon Kafar kasashen Afirka.

Magoya bayan 'yan wasan kasar Senegal sun tayar da hatsaniya ne bayan da 'yan wasan Ivory Coast suka jefa kwallaye biyu a ragar 'yan Senegal din a filin wasa na Dakar, al'amarin da ke zama barazana ga zuwan kasar tasu gasar ta Afirka.

Ivory Coast din ce dai ta lashe zagayen farko na wasan da ci hudu da biyu.

An bankawa wasu daga cikin kujerun da ke filin wasan wuta, sannan kuma an yi ta jifa da kwalabe da sauran abubuwa.

A shekarar 2008 ma an samu irin wannan tashin hankalin, lokacin da Gambia ta hana Senegal din zuwa gasar.

Sent from my BlackBerry wireless device from MTN

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.