BBC navigation

Algeria ta kashe wani fitattcen dan Al qaeda

An sabunta: 15 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 07:32 GMT

Shugaban kasar Algeria

Kasar Algeria ta ce dakarunta sun hallaka wani fitaccen dan kungiyar Al-Qaeda Boualem Bekai, a wani kwantan bauna da aka yi mishi a ranar juma'a.

Rahotanni sun ce shine jagoran kungiyar a yankin Maghreb wacce ke aiki a kasashe da dama da suka hada da Mali da Mauritania da Jamhuriyar Niger.

Jami'an kasar Algerian sun ce iyalan Boualem Bekai da aka fi sani da suna Khaled El Mig sun tabbatar da cewa shine aka kashe a lokacin da suka zo amsar gawarsa.

Al qaeda a yankin Almaghreb na dada zama barazana ga yankin Afrika ta Yamma, abinda ke dada jan hankalin kasashen duniya.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.