BBC navigation

Ghana ta tsare 'yan Ivory Coast 43 a wani sansanin 'yan gudun hijira

An sabunta: 15 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 20:07 GMT
Wani sansanin 'yan gudun hijira a Ghana

Ghana ta cafke wasu 'yan Kasar Ivory Coast

Hukumomin tsaro a Ghana sun tabbatar da tsare 'yan Kasar Ivory Coast su 43 a wani sansanin 'yan gudun hijira na farar hula dake kusa da birnin Takuradi a yammacin Ghanan, kuma ana zargin su na yaki ne a madadin tsohon Shugaban Kasar Laurent Gbagbo domin dagula kasar.

Hukumomin tsaron dai sun ce yanzu haka su na kan tantance mutanen domin zakulo wadanda ake zargin sune mayakan tsohon Shugaban Kasar

A baya dai Kasar Ivory Coast tayi zargin cewar Ghanan tana baiwa wadanda take zargin mayakan tsohon Shugaban Kasar ne mafaka

Dubun dubatar magoya bayan Tsohon Shugaba Gbagbo ne dai suka tsere zuwa Ghanan bayan zaben ShugabanKasar

A ranar talata ne ake saran wata Kotu a Ghanan zata yankewa wani tsohon minista a gwamnatin Laurent Gbagbo din hukuncin ko za a tusa keyar sa Kasar Ivory Coast, bayan da aka cafke shi a Kasar.

Kari a kan wannan labari

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.