BBC navigation

Ali Zeidan ya zama sabon Prime Ministan Libya

An sabunta: 15 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 07:27 GMT

Ali Zeidan


Majalisar dokokin kasar Libya ta zabi Ali Zeidan a matsayin sabon Prime Ministan kasar mako guda bayan da aka kori Prime Minista da ya gabace shi.

Mr. Ali Zeidan ya lashe zaben ne bayan fafatawa da abokin adawarsa wanda kuma Ministan gwamnatin kasar ne Mohamed Al-Harari, dake samun goyon bayan Jam'iyar Justice and Construction party wacce ke da alaka da kungiyar 'yan uwa Musulmi ta kasar masar.

Shi sabon Prime Minista nada kwanaki goma sha biyar ne don ya kafa majalisar zartarwar kasar, inda kuma ya yi alkawarin fara aiki gadan gadan.

Mr Ali Zeidan ya ce wannan gwamnatin zata rika mutunta dokokin kasa, ba zata kasance gwamnatin dake fama da rikice rikice ba.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.