BBC navigation

Malala zata samu lafiya! Inji Likitoci

An sabunta: 15 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 17:16 GMT
Asibitin da aka kai Malala, a Birmingham

Asibitin da aka kai Malala, a Birmingham

Likitoci sun ce matashiyar nan 'yan Pakistan, Malala Yusufzai, wadda 'yan Taliban suka harba a kaa bayan ta fara fafutukar samar da ilmi ga 'ya'ya mata, na iya samun damar warkewa.

Ana can ana aunata a wani asibitin da ya kware wajen lura da sojojin da suka samu raunuka a yaki.

Direktan Asibitin Sarauniya Elizabeth a Birmingham, Dr David Rosser, yace ba za'a dauko ta daga Pakistan ba, idan ba alamar za ta iya warkewa.

Jami'an Pakistan sun ce ta na bukatar a sake gyara wani bangare na kokon kanta; a kuma yi gyara a kwakwalwarta.

Malala dai, ta yi fice a fafitukar da take yi na ganin 'ya 'yan maata sun samu ilimin Boko a Pakistan.

A ranar Talatar da ta gabata ne, wani dan bindiga ya harbe ta a ka a lokacin da take kan hanyar komawa gida daga makaranta.

Likitoci a Peshawar na Arewa maso Yammaci Pakistan sun yi nasarar cire harsashin daga kokon kanta a makon jiya, daga nan kuma sai ta fara jinya a wani asibitin Sojojin da ke birnin Rawalpindi.

Yan Taliban ne dai suka dauki alhakin kai wa Malalan hari, kuma sun yi barazanar sake kai ma ta wani harin idan har ta rayu.

Kungiyar Taliban din ta ce ta kai ma ta harin ne saboda tana kokarin yada tsarin da ya raba addini da harkokin mulki.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.