BBC navigation

Tsoffin shugabannin Afrika sun gaza samun kyautar Mo a bana.

An sabunta: 15 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 17:34 GMT
Mo Ibrahim

Mo Ibrahim

Gidauniyar Mo Ibrahim wadda ke bada kyauta kan shugabanci nagari a Afrika, ta ce a bana babu wani tsohon shugaban kasar Afrika da ya cancanci samun wannan kyauta, wadda ake cewa ita ce mafi girma da ake baiwa tsoffin shugabannin Afrika.

Kyautar ta dala miliyan biyar, ya kamata a ce ana bada ita ne a kowace shekara, ga wani shugaba da aka zaba ta hanyar dimokradiyya, kuma ya bar gadon mulki a karshen wa'adin mulkinsa cikin ruwan sanyi.

Tun bayan fara bada wannan kyauta shekaru shidda da suka wuce, an samu tsoffin shugabanni uku da suka lashe kyautar.

Wadanda suka samu kyautar a baya sun hada da tsohon shugaban Cape Verde, Pedro Verona Pires, wanda ya samu kyautar a bara.

A shekara 2008 kuma Festus Mogae na Botswana ne ya samu.

Sai a 2007 lokacin da Joachim Chissano na Mozambique ya samu.

Wasu masu sharhi suna cewa ba su yi mamaki ba, ganin cewa babu wanda ya cancanci samun kyautar .

T

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.