BBC navigation

Clinton ta ce ita ce da alhakkin ofisoshin jakadanci

An sabunta: 16 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 07:22 GMT

Hillary Clinton

Sakatariyar harkokin wajen Amurka, Hillary Clinton, ta ce ita ce keda alhakin samar da tsaro a ofishin jakadancin Amurka dake Benghazi na kasar Libya inda aka kashe wani Jakadan Amurka a watan daya gabata.

Mrs Clinton ta shaidawa wani gidan talbijin na Amurka cewa tabbatar da tsaron lafiyar ma'aikatan Amurka dake aiki a ofisoshin Jakadancin kasar dake wasu kasashen duniya nauyi ne daya rataya a wuyanta ba fadar gwamnatin kasar ba.

Kisan da aka yiwa Jakadan Amurka Christopher Stevens, da wasu Amurkawa uku ya zamo wani babban abin muhawara a yayin da aka shiga makwonnin karshe na muhawarar da ake yi tsakanin 'yan takarar shugabancin kasar.

An dai farma ofishin Jakadancin Amurkar ne a Benghazi kan hoton batancin nan ga Annabi Muhammad Salallahu Alihi Wasallama.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.