BBC navigation

Tarihin shugaba Barack Obama

An sabunta: 17 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 14:16 GMT
Tarihin shugaba Barack Obama

Obama na neman Amurkawa su bashi karin lokaci domin cimma burinsa

Shugaba Barack Obama na neman Amurkawa su zabe shi a karo na biyu a daidai lokacin da tattalin arzikin kasar ke tangal-tangal, kuma kuri'un ra'ayin jama'a ke nuna cewa yana tafiya kan-kan-kan da Mitt Romney.

Sai dai Mr Obama yana da kwarin gwiwa: masu kada kuri'a na kaunarsa, kuma suna ci gaba da kaunarsa duk da cewa basu gamsu dari bisa dari ba da yadda yake gudanar da tattalin arzikin kasar.

Idan har zai iya shawo kan wadanda suka goya masa baya a 2008 su kara zabensa a watan Nuwamba, kuma ya gamsar da wadanda basu yanke shawara kan wanda za su zaba ba, cewa Romeny bai damu da su ba, to zai samu zagaye na biyu.

Mr Obama, wanda shi ne shugaban Amurka na farko bakar fata, ya gamu da mummunan matsalar tattalin arziki a shekaru hudun farko da ya shafe a kan mulki.

Barack Obama

Barack Obama

An haife shi 4 ga Agusta 1961 a Hawaii
Ya karanci shari'a a Harvard
Ya yi aikin lauya a Chicago
Ya zama Senator a jihar Illinois 1996-2004
An zabe shi Senator a Amurka a 2004
Ya doke Hillary Clinton a zaben cikin gida
An zabe shi shugaban kasa a 2008

Shi da sauran 'yan jam'iyyar Democrat, sun taka rawar gani.

Sai dai tattalin arzikin Amurka na ci ga ba da fuskantar matsala tun bayan da Obama ya karbi mulki: kirkirar sabbin guraban ayyuka na ci gaba da fuskantar koma-baya yayin da adadin marasa aikin yi ya ci gaba da kasancewa sama da kashi 8% cikin dari.

Dangantaka da Afrika

Bugu-da-kari, jam'iyyar Democrat ta fuskanci mummunan koma-baya a zaben 'yan majalisar da aka yi a watan Nuwamban shekara ta 2010, abinda ya baiwa Republican kwarin gwiwar tallata akidarsu ta ra'ayin rikau da kawo cikas ga shirye-shiryen shugaban.

An haifi Mr Obama ne a 1961, kuma aka sanya masa sunan babansa, wanda dan kasar Kenya ne da ya hadu da mahaifiyar Obama Ann, wacce farar fata ce daga Kansas, a lokacin da yake karatu a jami'ar Hawaii.

A lokacin da Obama yake karami, mahaifinsa ya rabi da shi bayan da auren mahaifan na sa ya mutu.

Sau daya suka kara haduwa bayan wata gajeriyar ziyara da mahaifin na sa ya kai Hawaii daga bisani.

A lokacin da Obama yake dan shekara shida, mahaifiyarsa ta auri wani mutumin Indonesia inda suka koma birnin Jakarta da zama.

Daga nan ne kuma Obama, wanda ake kira "Barry" ya koma Hawaii, inda ya taso a karkashin kulawar kakanninsa.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.