BBC navigation

Burtaniya ta ce ba za ta tesa keyar McKinnon zuwa Amurka ba

An sabunta: 16 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 19:07 GMT
Gary McKinnon

Gary McKinnon

Gwamnatin Birtaniya ta ce ba za ta tesa keyar dan kasarta, Gary McKinnon dake satar shiga bayanan sirri na Computer zuwa Amurka ba domin fuskantar tuhumar satar shiga cikin na'urorin computer na sojan Amurka.

Sakatariyar harkokin cikin gida ta Birtaniyan, Theresa May ta ce, Burtaniya ta yanke wannan shawarar ce bisa dalilan da suka shafi hakkinsa na bil'adama.

Wakilin BBC ya ce Gary McKinnon ya shaida masa cewar, ya yi satar shiga na'urorin Computer na ma'aikatar tsaro ta Pentagon da kuma hukumar binciken sararin samaniya ta NASA.

Masu gabatar da kara na Amurka sun zargi Gary McKinnon da yin mummunar barna ta hanyar satar shiga cikin na'urorin Computer na sojan Amurka.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.