BBC navigation

An raunata soja daya a wata musayar wuta a Potiskum

An sabunta: 17 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 15:56 GMT
damaturu

Mutane basu walwala a jihar Yobe, sai sojoji ke tabbatar da tsaro

An samu tashin bama-bamai da harbe-harben bindigogi da safiyar yau (Laraba) a garin Potiskum dake jihar Yobe a yankin arewa maso gabashin Najeriya.

Jami'an tsaro na hadin gwiwa wato JTF a birnin, sun ce bam din ya tashi ne a daidai lokacin da suka kai samame wani wuri da suke zargin maboyar wasu 'yan bindiga da ake zargin 'yan kungiyar nan ce ta Boko Haram.

Kakakin JTF din, Laftanar Lazarus Eli ya shaidawa BBC cewar, sun kai samamenne bayan wasu bayannan sirri da suka samu akan cewar akwai 'yan Boko Haram dake ajiye makamansu a wata maboya a garin Potiskum.

Laftanar Eli yace" an raunata soja daya a kafa, amma bansan adadin wadanda suka mutu ba a bangaren 'yan ta'adda ba, sai dai kuma mun samu makamai masu dinbim yawa a lokacin musayar wutar".

A garin Mubi na jihar Adamawa ma rahotanni sun ce an samu tashin bam da harbe-harben bindiga a kusa da wata kasuwa dake tsakiyar garin.

Sai dai jami'an tsaro a birnin Yola dake jihar ba suyi karin bayani ba game da batun.

Ko a ranar Alhamis ma, jami'an rundunar hadin gwiwa wato JTF a jihar Borno sun bayyana cewa sun kashe wasu wadanda suke zargin 'yan kungiyar Boko Haram ne su ashirin da hudu a wata arangama.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.