BBC navigation

Dubban mutane na makokin tsohon sarkin Cambodia

An sabunta: 17 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 15:41 GMT
makoki

Zaman makokin margayi Sarki Norodom Sihanouk a birnin Phnom Pehn

Dubban mutane dake makoki ne suka fito kan titunan Phnom Pehn, babban birnin Cambodia domin yin ganin karshe ga gawar tsohon Sarki, Norodom Sihanouk yayin da ake shirin kai gawar zuwa fadar masarautar kasar.

Mai dakin marigayin, da kuma dan sa, wanda shi ne sarki a yanzu, da kuma Pirayi Ministan kasar Hun Sen, sun yiwa gawar rakiya yayin da ake nuna ta ga jama'a cikin wani keke mai ruwan zinare.

Sarki Norodom Sihanouk ya mutu ne sakamakon ciwon zuciya ranar Litinin data wuce, a birnin Beijing na China, inda ya karasa sauran kwanakinsa a duniya.

Shi ne dai ya jagoranci Cambodia wajen samun 'yan cin kai daga Faransa cikin shekarun alif dari tara da hamsin.

Margayi Sarkin ya kasance magudu a cikin kasar Cambodia a lokacin yaakin daya barke da kuma kisan kiyashin daya biyo baya.

Kari a kan wannan labari

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.