BBC navigation

Nijer ta rage yawan kasafin kudinta

An sabunta: 17 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 21:01 GMT

Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta ce za ta rage kasafin kudinta na 2012 da kimanin kashi 7 bisa 100 na abinda ta shirya kashewa da farko.

Gwamnatin ta ce ta yi hakan ne saboda wasu matsaloli da ta samu wajen tattara kudaden daga wasu hukumominta da abokan arzikinta masu tallafa mata da kudaden.

Karo na ukku kenan dai da gwamnatin ke yi wa kasafin kudin na 2012 gyaran fuska.

Kudaden da gwamnatin tayi hasashen cewa za ta samu daga fannin man fetur da harajin kayayyakin da ake shigar dasu a kasar za su ragu sosai.

Sanarwar gwamnatin tace ana sa ran cewa za a samu kimanin CFA bilyan hudu a matsayin riba daga man fetur, kasa da CFA bilyan 35 da dubu 500 da aka yi tsammanin za a samu da farko.

A watan Julin da ya gabata gwamnatin ta kara yawan kudaden da take kashewa da kashi 10 bisa 100 don fuskantar matsalar fari da kuma na rikice-rikice akan iyakokinta.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.