BBC navigation

Rahoton kwararru ya zargi Rwanda da taimakawa 'yan tawaye

An sabunta: 17 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 07:17 GMT

'Yan tawayen M23


Wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya da wasu kwararru suka fitar ya ce kasar Rwanda ta ci gaba da goyon bayan 'yan tawaye a gabashin Jamhuriyar Dimokradiyar Congo har ta kai ga cewa Ministan tsaron kasar Janar James Kabarebe, shike Jagorancin 'yan tawayen.

Rahoton na sirri da kamfanin dillancin labaru na Reuters ya ce ya gani, ya zargi kasar Rwanda da ci gaba da taimakawa 'yan tawayen M23 da makamai da sauran kayayyakin soji harma da yi musu jagoranci, sai dai kasar Rwanda ta sha musanta wannan zargi.

Wakiliyar BBC ta ce kasashen duniya sun yi ta Allah wadai game da tashe tashen hankulan.

Rikicin da ake zargin kasar Rwanda da rurutawa ya sa Amurka da sauran kasashen turai janye tallafin da suke baiwa kasar Rwanda.

Kari a kan wannan labari

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.