BBC navigation

Wani Babban Jami'in Kungiyar Tarayyar Turai ya yi murabus

An sabunta: 17 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 07:35 GMT

John Dalli

Babban jami'i mai kula da bangaren kiwon lafiya na kungiyar tarayyar turai John Dalli ya ajiye mukaminsa bayan da aka danganta shi da wani yunkurin neman tabbatar da wata doka akan taba sigari.

Wannan dai ya biyo bayan koken da wani kamfanin sarrafa taba sigari na kasar Sweden ne ya yi cewa wani dan kasuwa daga Malta yayi kokarin samun kudade daga Mr Dalli, wanda shima dan asalin Maltan ne.

Kawo yanzu dai ofishin dake yaki da cin hanci da rashawa na tarayyar turai ya ce bai samu kwakkwarar shaidar data nuna cewa dan kasuwan ya sauyawa Mr Dalli ra'ayi ba, sai dai ofishin yace yana sane da wadannan batutuwa.

Mr Dalli dai ya yi watsi da wannan zargi, inda yace ya sauka daga kan mukaminsa ne saboda ya kare mutuncin sa.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.