BBC navigation

An dakatar da saida hannayen jarin kamfanin Google

An sabunta: 18 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 20:27 GMT
Kamfanin Google

An dakatar da saida hannun jarin Google

An dakatar da sayar da hannayen jari na kamfanin Google , bayan da su ka yi wata muguwar faduwa, lokacin da katafaren kamfanin intanet din ya bayyana sakamakon cinikin da ya yi cikin watanni ukun da su ka wuce, bisa kuskure.

Hannayen jarin kamfanin Google a New York sun fadi da kashi tara cikin dari, bayan da sakamakon ke nuna cewa ribar da kamfanin ya samu cikin watanni ukun da su ka wuce ta ragu da kashi daya cikin biyar.

Kamfanin ya ce wani kamfanin dab'i ne yayi garajen buga sakamakon farkon, wanda ya kamata a jira sai an rufe kasuwar hada-hadar hannayen jari ta New York, kafin a fitar da shi.

Ta wani bangare ana danganta raguwar ribar da kudaden da kamfanin ya kashe wajen sayen kamfanin kere-keren nan na Motorola.

Kari a kan wannan labari

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.