BBC navigation

Shugaba Jonathan ya gana da shugaban Nijer

An sabunta: 18 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 12:43 GMT
Goodluck Jonathan da Mahamadou Issoufou

Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya da Shugaba Mahamadou Issoufou na Nijar

Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya ya isa Yamai, babban birnin Jamhuriyar Nijar, don fara wata ziyarar aiki.

Yayin ziyarar tasa dai zai halarci taron Hukumar Hadin Gwiwa Tsakanin Najeriya da Nijar, wanda za su jagoranta shi da mai masaukinsa, Shugaba Mahamadou Issoufou na Jmahuriyar ta Nijar.

Daga cikin abubuwan da za a tattauna yayin taron akwai batun tsaro da cinikayya da kiwon lafiya da kuma kalubalen da ake fuskanta a kan iyakokin kasashen biyu.

Batun Mali ma na cikin abubuwan da za a tattauna a kansu.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.