BBC navigation

Merkel ta yi kira a baiwa EU cikakken 'yancin

An sabunta: 18 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 15:57 GMT
Shugabar Jamus Merkel da Francois Hollande na Faransa

Shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel ta yi kira da a baiwa Tarayyar Turai, cikakken 'yancin tsoma baki kan batun kasafin kudade a kasashe mambobin kungiyar.

Ta bayyana haka ne a jawabin da ta gabatar a majalisar dokoki, yayinda shugabannin tarayyar turan ke hallara domin wani taron koli a Brussels, da nufin samo hanyoyin kawo karshen matsalolin da kasashe masu amfani da kudin Euro suke fuskanta.

Misis Merkel ta kara da cewar "muna bukatar hanyoyin warware matsaloli wadanda za su rika sara suna duban bakin-gatari wajen tsoma baki a matakin tarayyar turan".

Misis Merkel ta kuma bukaci sauran shugabanni kada su yi saurin zura jiki wajen amincewa da sabbin dokoki kan sa ido a ayyukan banki, tana mai cewa, wajibi ne a fi baiwa inganci fifiko a kan samun sakamako cikin gaggawa.

Faransa da Spaniya na so ne a fara aiki da sabon tsarin daga nan zuwa watan Janairu.

Birtaniya wadda ita ce cibiyar kudade ta tarayyar Turai na so ne a bata wasu tabbaci na kare ikon da babban bankin Ingila yake da shi.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.