BBC navigation

Wani da ake zargi da ta'addanci a Amurka ya gurfana a kotu

An sabunta: 18 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 05:15 GMT

Jamiin FBI a kusa da Bankin Amurka

Wani mutum da ake zargi da yunkurin tayar da bam a babban bankin Amurka ya bayyana a gaban wata kotu dake birnin New York.

An dai cafke Quazi Nafis mai shekaru ashirin da daya dan kasar Bangaladesh ne a lokacin da yake kokarin tayar da wani abu da yake zaton cewa bama-bamai ne da aka makare su a wata mota kirar Bus.

Wani jami'in hukumar leken asiri na FBI ne dai ya shirya bama-baman na bogi bayan da wani mai samar musu da bayanan sirri ya shaida musu makarkashiyar da aka shirya.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.