BBC navigation

Najeriya: JTF ta ce ta kama ƙusa a ƙungiyar Boko Haram

An sabunta: 19 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 18:58 GMT

Abubakar Shekau, shugaban kungiyar Boko Haram

Rundunar haɗin gwiwa dake aikin samar da zaman lafiya a birnin Maiduguri tace ta cafke wani babban komandan kungiyar nan da aka fi sani da Boko Haram a birnin na Maiduguri jiya alhamis.

Rundunar ta JTF ta sanar da hakan ne a cikin wata sanarwa data fitar ɗauke da sa hannun kakakin ta Laftanal Kanal Sagir Musa.

Cikin sanarwar JTF tace, ta kama wani da ta ce ƙusa ne a ƙungiyar Boko Haram, mai suna Shu'aibu Muhammed Bama, a gidan wani dan majalisar dattawan Najeriya dake birnin Maiduguri.

Tun daga shekara ta 2009 ne dai birnin Maiduguri da kuma wasu sassan jihar Yobe suke fama da hare-haren da ake dangantawa da ƙungiyar ta Boko Haram.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.