BBC navigation

An tantance 'yan takarar shugabancin Ghana

An sabunta: 19 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 16:36 GMT

Shugaban a lokacin da yake rantsuwar kama mulki

Hukumar zaben kasar Ghana ta amincewa 'yan takarar jam'iyyu takwas su tsaya takarar shugabancin kasar a zaben da za'a yi cikin watan Disamba dake tafe.

Sai dai kuma hukumar zaben ta haramtawa 'yan takara shida tsayawa zaben bisa wasu dalili da suka shafi dokokin zaben kasar.

Uwargidan tsohon shugaban kasar, Jerry Rawlings wato Nana Konadu Agyemang Rawlings na daga cikin wadanda aka haramtawa tsayawa takarar shugabancin kasar.

An dai haramta mata tsayawa takarar ne saboda ta kasa cika ƙa'idojin da suka haɗa da miƙa takardun shiga takara akan lokaci.

Shugaba mai ci John Mahamma, na jam'iyyar NDC da kuma Nana Akufo Addo na jam'iyyar adawa ta NDP na daga cikin wadanda zasu tsaya takarar zaɓen.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.