BBC navigation

An ji karar tashin bama-bamai a Potiskum

An sabunta: 19 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 07:33 GMT

Wani waje da 'yan bindiga suka kai wa hari a Najeriya

A Najeriya, an shafe daren ranar Alhamis ana jin karar harbe-harben bindigogi da tashin bama-bamai a garin Potiskum da ke jihar Yobe.

Wadansu mazauna garin sun shaida wa BBC cewa tun karfe biyar da rabi na ranar aka fara harbe-harben har wayewar garin ranar Juma'a.

Sun kara da cewa lamarin ya sanya kowa ya shige gida domin tsira da rayuwarsa.

Ya zuwa yanzu dai babu cikakken bayani game da asarar dukiyoyi ko rasa rayuka da wannan lamari ya jawo.

BBC ta yi kokarin jin ta bakin jami'an tsaro amma wayoyin kakakin rundunar 'yan sandan jihar a kashe suke.

A ranar Talatar da ta gabata ma sai da wasu bama-bamai suka tashi a garin, inda jami'an tsaro na hadin gwiwa wato JTF a birnin suka ce bama-baman sun tashi ne a daidai lokacin da suka kai samame wani wuri da suke zargin maboyar wasu 'yan bindiga ne da ake zargin 'yan kungiyar nan ne ta Boko Haram.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.