BBC navigation

Somalia: hukumomi sun ƙwace makamai

An sabunta: 19 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 17:11 GMT

Mayaƙan Al Shabaab

Hukumomi a Somalia sun ce an ƙwace wani kwale kwale maƙare da makamai a arewa maso gabashin ƙasar da ake nufin kaiwa mayaƙan Al Shabaab masu kaifin kishin Islama.

Wani jami'i a yankin Puntland mai cin ƙwarya ƙwaryar gashin kan sa, yace an yi imanin cewa nakiyoyin dake ciki da alburusai da kuma bindigogi sun fito ne daga Yemen.

Majalisar ɗinkin duniya tunda farkon wannan shekarar tace, mafiyawancin mayakan Al Shabaab sun koma arewacin Somalia, bayan da dakarun tarayyar Afurka da na Somalian suka fatattake su daga wasu mahimman yankuna a kudancin ƙasar.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.