BBC navigation

An cafke tsohon Kakakin marigayi Kanal Gaddafi, Moussa Ibrahim

An sabunta: 20 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 20:06 GMT
Moussa Ibrahim

Rahotanni na cewa Moussa Ibrahim ya shiga hannu

Ofishin Fira Ministan Libya yace an cafke tsohon kakakin marigayi Kanal Gaddafi, kuma daya daga cikin mutanen da aka fi nema ruwa a jallo Moussa Ibrahim

Akwai dai rahotanni masu saba ma juna game da kama Musa Ibrahim, kakakin tsohuwar gwamnatin Marigayi Kanar Mu'ammar Gaddafi a Libya.

Kamun nasa dai, na zuwa ne yayinda ranar Asabar din nan ce ake cika shekara guda da kamawa, da kuma kashe Kanar Gaddafin.

Majiyoyi da dama sun tabbatar wa da BBC cewa tsohon kakakin gwamnatin Kanar Gaddafi , Musa Ibrahim ya shiga hannu.

Sai dai kuma akwai wasu majiyoyin na manyan hafsoshin sojin kasar da su ka ce ba za su iya tabbatar da gaskiyar labarin ba, kuma su na ma da ja a kansa.

Ofishin Fira ministan kasar ta Libya dai na nuna cewa an kama Musa Ibrahim ne yayinda yake kokarin tserewa daga garin Bani Walid.

Garin na Bani Walid ya kasance wata matattara a da, ta marigayi Kanar Gaddafi, kuma a 'yan makonnin da su ka wuce, wasu dakaru daga birnin Misurata mai makwabtaka da garin sun yi masa kofar-rago.

Kari a kan wannan labari

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.