BBC navigation

Ana zaben gwamna a Jahar Ondo a Najeriya

An sabunta: 20 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 15:12 GMT
Zabe a Najeriya

Ana zaben gwamna a Ondon Najeria

Yanzu haka ana can ana gudanar da zaben kujerar gwamna a jihar Ondo dake kudu maso yammacin Najeriya karkashin tsauraran matakan tsaro.

'Yan takara daga jam'iyyun siyasa 13 ne ke fafatawa a wannan zabe.

Manyan 'yan takarar kujerar gwamnan uku sun hada da gwamnan jahar mai ci, Olusegun Mimiko na jam'iyyar Labour da Rotimi Akeredolu na jam'iyyar 'Action Congress of Nigeria' da kuma Olusola Oke na jamiyyar PDP mai mulkin Kasar.

Zaben na kujerar gwamna a jihar Ondo dai, ya kasance wani zaben da ake hasashen zai iya zuwa da rikici da kuma zargin da jam'iyyun siyasa ke yi cewa ana shirin tafka magudi.

Sai dai hukumar zabe a Najeriyar ta kawar da duk wani zargi mai makamancin hakan.

Rahotanni dai ya zuwa yanzu na cewa zaben na gudana cikin lumana

Kari a kan wannan labari

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.