BBC navigation

Ba a kama dan Boko Haram a gidana ba - in ji Sanata Zanna

An sabunta: 20 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 07:46 GMT

Shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau

Dan Majalisar da ke wakiltar Borno ta Tsakiya a Majalisar Dattawan Najeriya, Ahmad Zanna, ya musanta zargin da rundunar hadin gwiwa , JTF ta yi cewa ta kama wani kwamandan kungiyar Boko Haram a gidansa.

Rundunar haɗin gwiwar da ke aikin samar da zaman lafiya ta ce ta cafke kwamandan kungiyar Boko Haram mai suna Shu'aibu Muhammed Bama ne a gidan wani dan majalisa a birnin Maiduguri ranar Alhamis - sai dai ba ta fadi sunan dan majalisar ba.

Sanata Zanna ya shaidawa BBC cewa: '' JTF sun bincika gidana ba su samu kowa ba, sai suka kama yaran gida suka fitar da su waje suka yi musu duka; kuma suka tambaye su ko sun san Shu'aibu Bama, yaran suka ce sun san shi. Daga nan ne daya daga cikin yaran ya kai su inda Shu'aibu ya ke. Amma ba a gidana suka kama shi ba''.

Sanata Zanna ya kara da cewa Shu'aibu Bama dan gidan 'yar uwarsa ne amma bai san ko dan kungiyar Boko Haram ba ne.

Ya ce a matsayinsa na dattijo ba zai boye duk wani mutum da ya san cewa dan kungiyar Boko Haram ba ne.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.