BBC navigation

Ma'aikatan Argentina za su fice daga jirginta da aka kama a Ghana

An sabunta: 21 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 07:10 GMT

Wani jirgin ruwan Argentina

Kasar Argentina ta umurci ma'aikatanta sama da dari uku su fice daga cikin wani jirgin ruwa da ake horas da mayakan ruwa wanda hukumomi suka kwace a kasar Ghana.

Matukin jirgin ruwan da wasu tsirarun ma'aikata ne kawai za su rage a cikin jirgin ruwan.

Ma'aikatar harkokin wajen kasar ta Argentina ta ce an keta hakkokin ma'aikatan jirgin ruwan bayan wani alkali a kasar Ghana ya ki amincewa a zuba wa jirgin ruwan mai - wanda ake bukata don sanyaya abinci da kuma amsa sakonnin gaggawa a cikin jirgin.

An kwace jirgin ruwan ne kimanin makonni uku da suka wuce bisa bukatar wani kamfanin zuba jari na yankin Caribbean.

Kamfanin dai yana neman kasar Argentina ne ta biya shi wasu kudade da yake bin ta bayan ta ki biyan bashin da ke kan ta shekaru goma da suka wuce.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.