BBC navigation

An zargi ministan Japan da yin hulda da miyagun mutane

An sabunta: 21 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 07:57 GMT

Keishu Tanaka

A kasar Japan, ministan Shari'a na fuskantar matsin lamba kan ya sauka daga mukaminsa, makwanni uku bayan an nada shi, saboda zargin da wata mujalla ta yi masa na yin alaka da kungiyoyin masu aikata miyagun laifuka.

Ministan mai suna Keishu Tanaka bai musanta yin hulda da kungiyoyin masu aikata laifuka ba, sai dai ya ce ya yi alaka da su ne shekaru 30 da suka gabata.

Da dama daga cikin 'yan kungiyoyin sun shaida wa wani fitaccen dan jaridar Amurka cewa Mista Tanaka ya daina hulda da kungiyar Yakuza da ke aikata laifuka ne shekaru biyu da suka gabata.

Matsin lambar da mujallar Yomiuri Shimbun ta yi masa ta sanya ministan ya je asibiti domin a duba lafiyarsa ranar Juma'a.

Firayim Minista na halin tsaka-mai-wuya

Wannan lamari ya jefa Firayim ministan kasar, Yoshihiko Noda, cikin halin tsaka-mai-wuya.

A baya, lokacin da jam'iyyar Liberal Democrat ke mulki a kasar, ba a yin suka ga shugabannin da ke da alaka da kungiyar Yakuza.

Hasalima, akwai 'yan kungiyar da suka zama 'yan majalisar dokokin kasar.

Sai dai jam'iyyar Firayim Minista Noda, watau Democratic Party of Japan tana adawa da kungiyar.

An zabe ta ne shekaru uku da suka gabata bayan ta yi alkawarin cewa za ta tsarkake fagen siyasar Japan, duk da yake masu sharhi a kasar sun ce ta gaza yin hakan.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.