BBC navigation

An bukaci majalisar China da kada ta kori Bo Xilai

An sabunta: 22 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 11:13 GMT
Bo Xilai

An yi kira ga majalisar dokokin China da kada ta kori Bo Xilai

Malaman jami'a da tsofaffin jami'an jam'iyyar Kwaminis ta China fiye da dari uku sun wallafa wata budaddiyar wasika suna kira ga majalisar dokokin kasar da kada ta kori dan siyasar nan da ya yi abin kunya, Bo Xilai, nan gaba a wannan makon.

Wasikar ta ce akwai ayar tambaya a shari'ance da kuma dalilai na siyasa a kan daukar wannan mataki [na korar Bo Xilai].

A watan da ya gabata aka kori Mista Bo—wanda ya yi tsamo-tsamo a abin kunyar siyasa mafi girma da China ta taba gani a shekaru da dama—daga jam'iyyar Kwaminis, sannan aka zarge shi da amfani da mukaminsa ta hanyar da ba ta dace ba da kuma cin hanci da rashawa.

Idan aka kore shi daga majalisar dokoki, za a tube masa rigar kariya daga tuhuma.

Ana gudanar da binciken aikata mugun laifi a kan Mista Bo sakamakon kisan wani dan kasuwar Burtaniya da aka yi bara.

Tuni aka garkame maidakinsa da wani tsohon jami'in 'yan sanda a gidan yari a dalilin wannan al'amari.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.