BBC navigation

Guinea Bissau ta zargi Portugal da yunkurin juyin mulki

An sabunta: 22 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 07:14 GMT

Sojojin Guinea Bissau

Gwamnatin rikon-kwarya a kasar Guinea Bissau ta yi zargin cewa kasar Portugal da ke goyon bayan tsohon Firayim Ministan kasar Carlos Gomez Junior ne suke da alhakin harin da aka kai a wani barikinta.

Portugal ce ta yi wa kasar ta Guinea Bissau mulkin mallaka.

An bindige wasu mutane bakwai da ke dauke da makamai a harin da aka kai bayan birnin Bissau, babban birnin kasar.

Sojojin da suka kifar da gwamnatin Firayim Minista Carlos Gomez Junior ne cikin watan Afrilu suka kafa gwamnatin rikon kwaryar.

Gwamnatin dai ba ta da goyon bayan kungiyar kasashen yammacin Afrika, ECOWAS da Tarayyar Turai.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.