BBC navigation

An hana shugaban Iran ziyarar wani gidan yari

An sabunta: 22 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 05:53 GMT
An hana  Ahmadinejad zuwa wani gidan yari

Ahmadinejad

A kasar Iran, an hana shugaba Ahmadinejad kai ziyara gidan yarin nan da ya yi kaurin suna wajen azabtar da jama'a, watau Evin da ke arewacin Tehran, babban birnin kasar.

Tun farkon wannan watan shugaban kasar ya nemi kai ziyara kurkukun jim kadan bayan an kame daya daga cikin na hannun damarsa bisa zargin batanci ga sauran shugabannin kasar ta Iran.

Sai dai a wani abin da ake ganin alamu ne na dusashewar ikonsa ga masu tsattsauran ra'ayi, jami'ai a gidan fursunan sun ki yarda su ba da izinin kai ziyarar, inda suka gaya wa shugaban kasar cewar abu ne da ba zai dace ba.

Sun ce wasu batutuwa muhimmai kamar mummunan halin da tattalin arzikin kasar ke ciki da hauhawar farashin kayayyaki, sune ya kamata su zamo abin da zai bai wa fifiko.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.