BBC navigation

An daure wasu masana kimiyya a Italiya

An sabunta: 22 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 20:09 GMT
Girgizar kasa a Italy

Girgizar kasa a Italy

Wata kotu a Italy ta yankewa wasu masana harkar girgizar kasa su shidda da wani jami'in gwamnati daurin shekaru shidda kowanensu, domin sun kasa yin hasashen irin tsananin girgizar kasar da za a yi kafin faruwarta a shekara ta 2009.


Kotun ta same su da laifin halaka mutane bada niyya ba.

An kuma haramta masu sake rike wani mukamin gwamnati har abada.


To saidai masu kare su sun nuna rashin gamsuwarsu da wannan hukunci.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.