BBC navigation

Mayaka masu kaifin kishin Islama na kwarara cikin arewacin Mali

An sabunta: 22 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 16:15 GMT
Garin Gao a arewacin Mali

Jama'a na kauracewa yankunan arewacin Mali

Rahotanni daga arewacin Mali na cewa daruruwan mayaka masu kaifin Kishin Islama ne ke ta kwarara cikin wasu garuruwa dake arewacin Malin da su ka hada da Kidal da kuma Gao.

Tuni dai wannan lamari ya sa yanzu haka magidanta a arewacin Malin su ma su ka soma kauracewa yankin zuwa Kasashen dake makwabtaka irin su Algeria domin kaucewa rikici.

Hakan kuma na faruwa ne a daidai lokacin da kungiyar ECOWAS take shirin daukar matakin soji a arewacin Malin domin fatattakar mayakan masu kaifin kishin Islama dake iko a yankin.

Wani magidanci a garin Kidal ya fadawa BBC cewa mayakan na fitowa ne daga garuruwan dake iyaka da Malin da kuma wasu Kasashe

Ya kara da cewa akasarin su na magana ne da harshen turanci kuma ya ce jajaye ne kamar larabawa.

Ba a dai san dalilin kwararowar su a wannan lokaci ba, amma masu sharhi na ganin cewar maiyiwuwa hakan na da alaka da matakin sojin da ake shirin dauka a Malin

Kari a kan wannan labari

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.