BBC navigation

An samu raguwar fashin teku a duniya

An sabunta: 22 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 16:50 GMT
Fashin teku

Matsalar Fashin teku ta ragu a duniya

Hukumar kula da zirga zirgar jiragen ruwa ta duniya tace an samu raguwar matsalar fashi akan teku sosai tun daga shekara ta 2009.

Hukumar ta alakanta raguwar alkaluman aikace aikacen fashi akan tekun ga raguwar da aka samu sosai na yawan hare haren da 'yan fashin tekun Somalia suke kaddamarwa daga kusan 200 a bara zuwa 70 a shekarar 2012.

Amma hukumar ta jaddada cewa sai an tashi tsaye wajen kauda matsalar gabakidayan ta

To sai dai yayin da wannan matsala ke raguwa a gabashin Afirka, a yammacin Afirka kuwa lamarin ba haka yake ba

Hukumar ta kuma ce an samu karuwar abkuwar fashi akan teku ta gabar tekun Guinea

Ta kuma ce mummunan farmaki 'yan fashi akan teku ke kaiwa ta gaba daga Najeriya da Benin da kuma Togo

Kari a kan wannan labari

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.