BBC navigation

An kai hari a kan jami'an tsaro a Potiskum

An sabunta: 22 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 06:40 GMT

Jami'an tsaro a Najeriya

Rundunar samar da tsaro a garin Potiskum da ke jihar Yoben Najeriya sun ce ma'aikatansu sun samu raunuka a ranar Lahadi lokacin da wasu 'yan bindiga suka kai harin bom kan wata motar sojoji inda motar ta kama da wuta.

Kakakin rundunar, Latfanal Lazaruz Eli, ya shaidawa BBC cewa biyu daga cikin ma'aikatansu ne suka samu raunuka lokacin da aka jefa bom a kan motarsu da ke tafiya a wani yanki na garin.

Ya kara da cewa sun aike da karin sojoji zuwa garin domin karawa rundunarsu karfi.

Wadansu mazauna garin sun shaidawa BBC cewa sun kwashe sa'o'i da dama suna jin karar harbe-harben bindigogi da tashin bama-bamai.

Sun kara da cewa da dama daga mazauna birnin na ficewa daga cikinsa domin tsira da rayukansu.

Potiskum na daga cikin garuruwan da ke fama da hare-hare da ake zargin 'yan kungiyar Boko Haram ne ke kai wa.

Mutane da dama ne suka mutu sakamakon hare-haren.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.