BBC navigation

Obama da Romney: Manufofin hulda da kasashen waje

An sabunta: 22 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 17:55 GMT

’Yan takarar shugabancin Amurka, Barack Obama da Mitt Romney na daf da sake fafatwa a muhawararsu ta karshe ranar 22 ga watan Okotoba; jigon muhawarar shi ne Manufofin Hulda da Kasashen Waje.

Ga kadan daga cikin mahangarsu wadda aka tattare bisa la’akari da furucinsu na baya-bayan nan.

Iran

Manyan batutuwa: Shirin nukiliya na Iran, barazanar samar da makamin nukiliya, yiwuwar barkewar yaki da kuma hasashen Isra’ila za ta yi gaban kanta ta kai hari.

 • Abin da Obama ya ce: “Kasashe masu karfi da shugabannin kasa masu karfi kan tattauna da abokan hamayyarsu”. Matsayinsa: Bai dace ba a kyale Iran ta mallaki makamin nukiliya. Bai kawar da yiwuwar daukar ko wanne irin mataki ba amma a zahiri ya fi kaunar warware matsalar ta hanyar tattaunawa ko kuma takunkumi. Ko da yake yunkuri na farko na tuntubar Iraniyawan bai yi nasara ba, ga alama takunkumin da kasashen duniya suka kakabawa Iran na yin tasirin da gwamnatin Obama ke fatan gani.

 • Abin da Romney ya ce: “...idan kuka zabe ni shugaban kasa, ba za su mallaki makamin nukiliya ba...”. Matsayinsa: Ya fi murza gashin-baki. Ya kuma tsaya kai-da-fata a kan cewa kada a kyale Iran ta mallaki makamin nukiliya amma ya dora a kan haka da nuna adawarsa ga barin ta ta mallaki ko wanne irin shiri na nukiliya. Ya yi watsi da tattaunawa, amma ya yi ikirarin zai nemi a kakabawa Iran takunkumin da ya fi yanzu tsauri. Sai dai kuma ya yi amanna cewa ya kamata a fito karara a yiwa Iraniyawa barazanar daukar matakin soji.

Isra'ila

Manyan batutuwa: Matsugunan Yahudawa a yankunan da Isra’ila ta mamaye, tattaunawar samar da zaman lafiya tsakanin Isra’ila da Falasdinawa, baiwa Falasdinawa kasarsu ta-kansu.

 • Abin da Obama ya ce: “Kudurinmu na tabbatar da tsaron Isra’ila ba zai taba girgiza ba, haka ma yunkurinmu na samar da zaman lafiya”. Matsayinsa: Ya jaddada kudurinsa na tabbatar da tsaron Isra’ila, amma kuma yana ganin halin da ake ciki ba mai dorewa ba ne, don haka yake goyon bayan warware rikicin ta hanyar baiwa Falasdinawa kasarsu. Ya bukaci kungiyar Hamas ta amince da hakkin Isra’ila na wanzuwa sannan ya yi watsi da tashin hankali. Yana adawa da gina matsugunan Yahudawa a yankunan da Isra’ila ta mamaye, batun da ya jawo rashin jituwa tsakaninsa da Firayim Minista Benjamin Netanyahu. Obama ya hakikice cewa akwai kyakkyawar dangantaka a tsakaninsu amma a zamaninsa bai ziyarci Isra’ila ba.

 • Abin da Romney ya ce: “Kashin bayan samun zaman lafiya shi ne Isra’ila ta samu tabbacin kasancewa cikin tsaro”. Matsayinsa: Ya kwatanta Isra’ila da kawar Amurka mafi kusanci sannan ya soki lamirin Obama a kan yadda ya nesanta kansa da ita. Ba ya adawa da gina matsugunan Yahudawa kuma yana so a fi mayar da hankali a kan habaka tattalin arzikin yankunan Falasdinawa a maimakon kara musu karfi a siyasance. Ya nuna shakku a kan dorewar shirin kirkirar kasar Falasdinu. Ya ziyarci Isra’ila yayi yakin neman zabae amma kuma an ambato shi yana cewa “Sam sam Falasdinawa ba su da sha’awar samun zaman lafiya”.

Kasashen Larabawa/Musulmi

Manyan batutuwa: Abin da ya biyo bayan juyin juya-halin kasashen Larabawa, rikicin kasar Syria da fim din kiyayya da Musuluncin nan da ya harzuka tashe-tashen hankula a kan ofisoshin jakadancin Amurka.

 • Abin da Obama ya ce: “Amurka da Musulunci ba sa zaman doya da manja, don haka bai kamata su rika gasa da juna ba”. Matsayinsa: FTun farkon hawansa mulki, Obama ya yi yunkurin kara fahimtar juna da kasashen Larabawa da na Musulmi. Ya goyi bayan sauye-sauyen dimokuradiyya a yankin sannan ya fitar da wani shiri na zuba jari da bayar da lamuni don samar da ababen more rayuwa da ayyukan yi. Ya shiga hadin gwiwar kungiyar tsaro ta NATO wadda ta rika kai hari a kan Muammar Gaddafi a Libya sannan ya amince da tsauraran takunkumin karya tattalin arziki a kan Syria yana kira ga Shugaba Bashar al-Assad ya mika mulki ba tare da bata lokaci ba. Dangane da fim din nan na kiyayya ga Musulunci kuma ya kare ’yancin fadin albarkacin baki sannan ya yi Allah-wadai da tashe-tashen hankulan da fim din ya haddasa.

 • Abin da Romney ya ce: “Gwamnatin Romney za ta yi aiki tukuru don tabbatar da cewa reshe bai juye da mujiya ba a juyin juya-halin kasashen Larabawa”. Matsayinsa: Yana kallon juyin juya-halin kasashen Larabawa a matsayin wata kyakkyawar dama ta kawo sauyi amma yana dari-dari a kan yiwuwar ya kasance budewar kofa ga magautan Amurka a yankin. Ya gamsu da rawar da Amurka ta taka a matakan sojin da aka dauka a Libya amma bai gamsu da lokacin da aka yi hakan ba. Ya soki lamirin “rashin katabus” din Obama a Syria kuma zai so ya ga Amurka da kawayenta sun tallafawa ’yan adawar Syria da makamai. Bai goyi bayan daukar matakin soji nan take ba amma ya ce wajibi ne Amurka ta tsoma baki don hana yaduwar makami mai guba. Ya yi kakkausar suka a kan martanin shugaban kasa dangane da hare-haren da aka kai a kan ofisoshin jakdancin Amurka.

China

Manyan batutuwa: Tattaunawa da kuma bijirewa habakar tattalin arzikin China da yaduwar tasirinta a siyasance da kuma karuwar karfinta ta fuskar soji, da cike gibin cinikayya, da takaita harkokin cinikayya da manufofin kuddae masu cike da cece-kuce, da kuma kare hakkokin bil-Adama.

 • Abin da Obama ya ce: “Ba burin Maurka ba ne ta takura China... karuwar karfin China da habakarta ka iya zama amfani ga kasashen duniya”. Matsayinsa: Ya bukaci cude-ni-in-cude-ka yana mai amanna da bin hanyar lalama, amma kuma ya caccaki China saboda zargin tana kayyade darajar kudadenta tana kuma aikata son zuciya a harkar cinikayya; ya ba da sanarwar kafa wata hukuma don binciki wadannan aika-aika. Ya damu da yadda tasirin China ke karuwa a nahiyar Asiya sannan ya tsara wani shiri na kara karfin rundunar sojin ruwan Amurka a yankin. Ya yi nasarar tsallakar da wani dan adawar China wanda ya tsere dag inda ake yi masa daurin talala.

 • Abin da Romney ya ce: “Idan kana shakkar tashi ka tunkari China, to China za ta murkushe ka”. Matsayinsa: Yana da burin ganin an dauki matakan ba-sani-ba-sabo, ciki har da kara karfin soji sosai a yankin Pacific, da kara karfin dangantaka da India da sauran kawayen Amurka na yankin, da karfafa harkar kare hakkokin bil-Adama da kuma tilasta wa China ta rika yin adalci a manufofinta na cinikayya. Ya kuma yi watsi da kamfen da Obama yake yi a Kungiyar Cinikayya ta Duniya dangane da halayen China, yana mai cewa ya yi kadan kuma ya zo a makare. Ya kan yi magana a bainar jama’a a kan zargin sarrafa darajar kudade da kuma satar shiga kwamfiyutocin gwamnati da kamfanonin Amurka. Ya yarda da kasancewar China wata kasa mai karfin arziki wacce za a iya yin cinikayya da ita amma bisa tsauraran sharudda.

Rasha

Manyan batutuwa: Kara dankon zumunci bayan komawar Vladimir Putin kan kujerar shugabanci, yarjejeniyar rage makaman nukiliya, hada karfi da karfe don taka wa Iran birki da kuma tilasta al-Assad sauka daga mulki.

 • Abin da Obama ya ce: “...ba yadda za a yi ka kira Rasha babbar makiyiyarmu sai dai idan akwai tawayar yakin cacar-baka a kwakwalwarka”. Matsayinsa: Ya sabunta dangantaka tsakanin Amurka da Rasha sannan ya rattaba hannu a kan sabuwar yarjejeniyar rage makaman nukiliya. Ya mara baya ga shigar Rasha Kungiyar Cinikayya ta Duniya, al’amarin da ya taimakawa kasashen biyu suka daidaita huldar cinikayya a tsakaninsu. Ya cimma matsaya da Moscow dangane da takunkumin da aka kakabawa Iran, amma ya kasa daidaitawa da Rasha a kan matakin da ya kamata a dauka a kan Syria kuma gwamnatinsa ta zargi Rasha da aikewa gwamnatin Assad jiragen yaki masu saukar ungulu.
 • Abin da Romney ya ce: “Ba ko tantama Rasha ce abokiyar hamayyarmu ta farko. Suna fada a madadin duk miyagun mutane a duniya”. Matsayinsa: Ya ce zai “sabunta sabuntawar”. A yakin neman zabensa ya fayyace wani shiri na hana abin da ya kira halayyar nuna karfi da kuma karfafa dimokuradiyya da sauye-sauyen tattalin arziki. Ya ce zai fito fili y kalubalanci gwamnatin Rasha a kan manufofinta na kama-karya. Yana ganin Obama ya mayar da hankali fiye da kima a kan takaita yaduwar makamai. Ya yi adawa da shigar Rasha Kungiyar Cinikayya ta Duniya sannan ya zargi Moscow da yin kafar ungulu ga kudurorin Majalisar Dinkin Duniya a kan Iran da Syria.

Latin Amurka

Manyan batutuwa: Takunkumin da Amurka ta kakabawa Cuba, takaita yaduwar makamai, safarar miyagun kwayoyi da tashe-tashen hankula a kan iyaka da Mexico, karfafa cinikayya da kasashe duk da sababbin kungiyoyin da aka samu baya ga abokan cinikayya, tunkarar gwamnatoci masu ra’ayin gurguzu da adawa da Amurka.

 • Abin da Obama ya ce: “Latin Amurka yanki ne mai ci gaba, wanda ke alfahari da ci gabansa kuma a shirye yake ya kara taka rawa a al’amuran duniya...yana kuma da muhimmanci ga ci gaba da tsaron Amurka fiye da ko wanne lokaci a baya”. Matsayinsa: Matsalolin cikin gida da na waje sun sha kan manufar Obama a nan, ko da yake ya yi alkawarin kulla alaka da yankin. Ya sassauta takunkumin hana zirga-zirga zuwa Cuba amma bai yi sauyi ba a kan takunkumin da aka kakabawa kasar shekara da shekaru. Ya ci gaba da Tsarin Merida wanda George W. Bush ya kirkira; shirin da ya tanadi jami’an Amurka shiga yakin da ake yi da miyagun kwayoyi da makaman da ke karakaina a kan iyakar Amurka da Mexico, sannan ya rattaba hannu a kan yarjejeniyoyi biyu na cinikayya da Colombia da Panama, wadanda George Bush ya assasa.
 • Abin da Romney ya ce: “Zan kaddamar da wani kamfe na habaka huldar tattalin arziki a Latin Amurka, sannan in bambanta tsakanin alfanun dimokuradiyya da jari hujja da mugunyar tsari irin na Venezuela da Cuba”. Matsayinsa: Manufar Romney a yankin ta yi kama da ta Obama don kuwa alamu na nuna cewa da a kan kujerar shugabanci yake ba zai baiwa yankin muhimmanci ba. Amma kuma ya bayyana cewa zai taka muhimmiyar rawa a Latin Maurka ta hanyar goya baya ga abokan Amurka masu bin tsarin dimokuradiyya. Matsayinsa shi ne cewa Venezule da Cuba—wadanda ya ce suna jagorantar mummunar kiyayyar Amurka a yankin, ya kuma yi gargadin cewa abokan burmin Iran ne da kungiyoyin masu tsattsauran ra’ayi irinsu Hizbullah—suna barazana ga ci gaban kawancen da aka samu a yankin ta fuskar tsaro, da dimokuradiyya, da tattalin arziki. Yana shirin kaddamar da abin da ya kira Yekuwar Habaka Tattalin Arzikin Latin Amurka.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.