BBC navigation

Darakta Janar na BBC zai fuskanci tambayoyin 'yan majalisar dokokin Birtaniya

An sabunta: 23 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 08:10 GMT
Tsohon mai gabatar da shirye-shiryen BBC Jimmy Saville

Tsohon mai gabatar da shirye-shiryen BBC Jimmy Saville

Darakta Janar na BBC, George Entwistle zai fuskanci tambayoyi daga kwamitin Majalisar Dokokin Birtaniya, kan matakin da BBC din ta dauka a bara na jingine bincike kan zargin lalata da kananan yara da ake yiwa tsohon mai gabatar da shirye-shiryen gidan talabijin na BBC Jimmy Saville.

A bara ne dai Mr Saville ya rasu, amma kuma yanzu haka 'yan sanda na ci gaba da bincike kan zarge-zarge da dama da ake yi a kansa.

An kuma zargi BBC da yin watsi da rahoton saboda tana shirin watsa shirye-shiryen yabo kan tsohon mai gabatar da shirye-shiryen nata.

'Yan majalisar za su bukaci amsa kan wata muhimmiyar tambaya, shin me ya sa shirin BBC na Newsnight ya jingine rahoton binciken kan Jimmy Saville.

BBC dai ta musanta cewa akwai matsin lamba kan shirin na Newsnight na ya jingine rahoton, saboda ma'aikatar na wani yunkuri na gabatar da shirye-shiryen karrama tsohon sanannen mai gabatar da shirye-shiryen nata a cikin watan Disambar bara.

BBC din ta ce an jingine binciken ne saboda wasu abubuwa da suka shafi dokoki da ka'idar aikin jarida, ba wai don yin rufa-rufa kan halayyar tsohon tauraron ba.

Amma kuma 'yan majalisar na son su san takamaiman masaniyar da Mr George Entwistle da sauran manyan manajojin suke da ita game da yanayin binciken na Newsnight, kana ko kuma akwai wani abu da yayi tasiri cikin shirin.

Ko shakka babu ana kallon wannan a matsayin tsaka mai wuya ga BBC.

Lamarin ya haifar da ayoyin tambaya ba wai a kan yadda aka kyale Jimmy Savile yayi ta tafka ta'asa kamar yadda yayi a cikin shekaru da dama ba, har ma da yanayin yadda aikin yada labaran yake a ma'aikatar da ma su kansu shuwagabannin.

Sent from my BlackBerry wireless device from MTN

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.