BBC navigation

Shugaban cibiyar nazarin tantance afkuwar hadura a Italiya ya yi murabus

An sabunta: 23 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 20:36 GMT
Girgizar kasar da aka yi a L'Aquila

Girgizar kasar da aka yi a L'Aquila

Shugaban cibiyar nazarin tantance afkuwar hadura ta Italiya ya yi murabus, bayan da aka yankewa wasu abokan aikansa su bakwai hukuncin dauri a gidan kaso, saboda kasa bayyana girman girgizar kasa, kwanaki kadan kafin bala'in da ya auku a L'Aquila a shekara ta 2009.

Luciano Miani ya ce akwai kuskure a hukuncin na kotun.

Masana kimiya shida da wani jami'ian gwamnati ne aka yankewa hukuncin daurin shekaru shida kowannensu a gidan yari, bayan kotun ta same su da laifin kisan kai ba da nufi ba, sakamakon bada bayanan da ba su yi daidai ba.

Girgizar kasar dai ta janyo a garin na L'Aquila dai ta haddasa rasuwar mutane fiye da dari uku .

Shugaban kungiyar kimiya ta Italiya, Stefano Cresta, ya ce a irin wannan lokacin, ba a Italiya ba kadai ko ma a ko' ina a duniya, ba zai yiwu ba a iya tattance karfin girgizar kasa kafin ta faru.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.