BBC navigation

An kaddamar da kamfe na yaki da satar danyen mai a Najeriya

An sabunta: 23 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 08:26 GMT
Taswirar Najeriya

Taswirar Najeriya

Masu kamfen sun ce kashi 90 cikin dari na danyen man da ake sace wa daga kasar ana sayar da shi ne a kasuwannin duniya, inda matatun man fetur a yankin Balkans da Singapore ke kan gaba wajen sayen man.

An dai yi kiyasin cewa kimanin gangar mai 180, 000 ake sacewa daga Najeriyar a kowacce rana.

Wani tsohon jami'in diflomasiyya kuma tsohon mai baiwa shugaban kasar shawara Patrick Dele Cole shi ne ke kan gaba wajen yaki da ta'adar.

Ya ce "ina ganin ya kamata a aikewa wadanda suka yi kazamin arziki ta wannan hanya su san cewa ruwa fa ya kusa karewa dan kada''.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.