BBC navigation

Sojojin Isra'ila sun hallaka mutane uku

An sabunta: 24 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 12:56 GMT

sarkin Qatar a Gaza

Wani hari da sojojin Isra'ila suka kai Zirin Gaza ta sama ya kashe 'yan bindigar Hamas akalla uku ya kuma raunata wadansu da dama.

Sojin Isra'ilan sun ce sun kai wa zaratan Hamas din harin ne a daidai lokacin da suke kokarin harba makaman roka cikin Isra'ila.

Isra'ila ta ce kimanin makamai masu linzami hamsin ne suka fada a yankin, inda suka ji wa mutane uku mummunan rauni. An kulle makarantun da suke dukkan bangarorin yankin saboda fargabar za a a kai wani harin.

Isra'ila ta kai harin ne kwana daya bayan ziyarar da Sarkin Qatar ya kai Zirin na Gaza, wadda ita ce ta farko da wani shugaba na wata kasar waje ya kai yankin tun bayan da Hamas ta kama mulki shekaru biyar da suka wuce.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.