BBC navigation

An kwashe wasu ma'aikatan Jirgin ruwan Argentina daga Ghana

An sabunta: 24 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 16:29 GMT

Ma'aikatan Jirgin ruwan horos da mayakan ruwa na kasar Argentinan da aka kwace fiye da makunni 3 da suka wuce a Ghana a sakamakon wata takaddama kan bashi na kan hanyarsu ta zuwa gida

An hana jirgin ruwan barin tashar jiragen ruwa ta Tema a farkon watan Oktoba a lokacin da wata kotu a kasar ta yanke hukuncin da ya bai wa wani asusun hada hadar kudi da wani Biloniyan Amurka ke goyon baya.

Mayakan ruwa 280 ne za su bar jirgin -- mai suna Libertad -- wani katafaren jirgi -- bayan dadewarsu a Ghana.

Matukin da kuma ma'aikatan jirgin da yawa za su ci gaba da zama a cikinsa.

Za su tashi ne a wani jirgin saman kamfanin jiragen sama na Faransa da aka dauka haya.

An dai yi watsi da wani shirin farko na cewar za su tashi ne da wani jirgin saman Argentina saboda tsoron cewar za a iya rike shi kansa jirgin saman a cikin takaddamar bashin.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.