BBC navigation

An hana 'yan Okada bin wasu hanyoyi a Legas

An sabunta: 24 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 16:52 GMT
Jahar Lagos

Jahar Lagos

Masu sana'ar Okada a jahar Legas sun gudanar da wata zanga zanga bisa hanasu sana'arsu a wasu titunan jahar.

Gwamnatin jihar Lagos dai ta haramtawa masu hayar Babura bin wasu hanyoyin jihar guda 475.

Mataki da tuni ya fara haifar da karancin ababan hawa, inda jama'a suka fara fuskantar matsananciyar wahala wajan zirga zirga a wadannan wurare.

Gwamnatin jihar Lagos dai tace ta kafa wannan dokar dan magance yawan haddura da ake samu a da ake zargin 'yan Okadan na haddasawa da kuma fashi da makami.

Sai dai 'yan Okadan sun musanta wannan zargi suna masu cewa wasu masu baruran ne ke wadannan abubuwa suna goga musu kashin kaji.

Miliyoyin mutane ne dai a jahar ta Legas suka dogara da sana'ar ta Okada imma wajan zirga zirga ko kuma neman abincin da zasu ci da Iyalinsu.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.