BBC navigation

Sojojin sa kai na kasashen waje sun shiga arewacin Mali

An sabunta: 24 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 07:41 GMT
Sojojin kasar Mali

Sojojin kasar Mali

Al'ummomin da ke daya daga daga cikin manyan yankunan da 'yan tawaye masu kishin Islama ke rike da su a arewacin Mali sun ce sun ga manyan motoci dauke da sojojin sa kai na 'yan kasashen waje sun hallara a yankin, yayinda kasashen duniya ke kara nuna damuwa akan halin rashin kwanciyar hankalin da ake ciki a Malin.

Magajin garin Gao Sadou Diallo , wanda ya tsere zuwa babban birnin kasar, Bamako, ya ce sababbin sojojin sa kan sun hada da kusan dakaru 100 da ake kyautata zaton sun fito ne daga yankin yammacin Sahara da kuma Algeria.

A baya-bayan nan dai gwamnatocin Birtania da na Jamus, su ne suka yi tayin bada gudummawarsu ga shirin samar da rundunar soji ta kasashen duniya da zata yi aikin kawar da 'yan tawayen na Mali.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.